✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Adadin matan da ke zuwa makaranta ya karu a Kano’

An sami nasarar ce saboda bullo da darussa kan jinin al’ada a Jihar

Makantu a Jihar Kano sun sami karin adadin yaran da ke zuwa makaranta, musamman a tsakanin dalibai mata.

Daraktan Tsare-tsare, Bincike da Kididdiga na Ma’aikatar Ilimin Jihar Kano, Munzali M. Mustapha ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa kan ilimin mata da Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) a Kano.

A cewarsa, bincike ya nuna a baya, dalibai mata, musamman a yankunan karkara kan kauracewa makarantunsu a duk lokacin da suke jinin al’ada, amma a yanzu lamarin ya canza.

Daraktan ya kuma ce akasarin irin wadannan daliban ba sa komawa makarantun saboda irin tsangwamar da suke fuskanta daga sauran dalibai, lamarin da ya ce yana matukar yi wa harkar iliminsu illa.

Munzali ya ce kirkiro da darasi kan yadda mata za su kula da tsaftarsu yayin jinin al’ada ya rage tsangwamar sosai, lamarin da kuma ya ce ya kara hatta adadin daliban a cikin makarantun Jihar.

Da yake nasa jawabin, Shugaban ofishin UNICEF a Kano, Rahama R. Farrah, ya ce shirin ilimantar da ’ya’ya mata wanda Hukumar Kasashen Rainon Ingila (FCDO) take daukar nauyi ya bullo da shirye-shiryen da ke tabbatar da mata na zuwa makaranta.

Ya ce wasu daga cikin shirye-shirye sun hada da darasi kan tsaftar jinin al’ada ga dalibai mata da kuma aikin samar da kayayyakin tsafta a makarantun.

Sai dai wasu alkaluman da UNICEF din ta fitar sun nuna cewa yanzu haka a Najeriya, akwai yara kumanin miliyan 18.5 da ba sa zuwa makaranta.

Ya ce kusan kaso 60 cikin 100 na wannan adadin mata ne, lamarin da ke nuni da cewa kusan ’yan mata miliyan 10 ne ke nan ba sa zuwa makaranta a Najeriya.

Shugaban ya kuma koka cewa mafi yawa daga cikin adadin wadannan matan daga Arewacin Najeriya suka fito, lamarin da ya ce yana kara tazarar da ke akwai tsakanin maza da mata a wajen zuwa makaranta.