✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin ficewa ta daga PDP -Dogara

Yana zargin karya alkawarin zabe da almubazzaranci a jiharsa.

Tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya bayyana makasudin sake komawarsa jam’iyyar APC.

Dogara, wanda ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa APC a ranar Juma’a ya koka kan gazawar shugabanci a jiharsa ta Bauchi karkashin jagorancin gwamna Bala Mohammed.

A wasikarsa shugaban PDP na mazabarsa ta Bogoro ‘C’, Dogara ya ce ba zai ci gaba da zura ido ana yin kuskure ba tare da ya yi magana ba, idan kuma ya bukaci a gyara sai a ce ya yi rashin da’a.

Ya ce zai kasance dan siyasa mara alkibla idan har ya ga ana yin ba daidai ba ya ki yin magana, kamar yadda ya yi ga gwamnatocin Isa Yuguda da Mohammed Abubakar a jihar.

A cikin wasikar, Dogara ya ce, “Na yanke shawarar yin tsokaci kan wadannan abubuwan ne saboda alkawarin da muka yi na kafa gwamnatin adalci a Bauchi”.

Ya kuma yi zargin facaka da kudaden kananan hukumomi, gaza cika alkawuran yakin neman zabe da kuma zargin ciyo bashin sama da Naira biliyan hudu da rabi da aka karkatar da su zuwa asusun wani kamfani da ba na gwamnati ba.

“A kan wane dalili za a damka ragamar tafiyar da albashin ma’aikatan jihar Bauchi ga wani kamfani mai zaman kansa. Me ya sa ake kara kudaden kwangila. Me yasa ba a mutunta sarakuna kamar yadda muka yi alkawari a lokacin yakin neman zaben PDP?

“A kan wadannan dalilan da ma wasu, na yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar PDP domin samun damar ci gaba da gwagwarmayar tabbatar da gwamnati mai adalci a jihar Bauchi”, inji Yakubu Dogara.

Tuni dai shugaban jam’iyyar ta APC reshen jihar Bauchi Alhaji Uba Nana ya ce shirye-shirye sun yi nisa na gangamin tarbar Dogara nan ba da jimawa ba.

Sauya sheka a jinin Dogara yake – PDP

To sai dai kakakin PDP a jihar, Yayanuwa Zainabari ya ce zarge-zargen da Dogara ke wa Gwamna Bala Mohammed ba su da asali.

Ya kuma dage kan cewa gwamnan na gudanar da gwamnati da ke mutunta kowa tare da gudunmawar duk masu ruwa da tsaki a jihar ciki har da shi Dogaran.

Ya yi zargin cewa sauya sheka a siyasance abu ne da ke a jinin tsohon Kakakin Majalisar Wakilan.