Mene ne amfanin man goge hannaye na “Hand Sanitiser? Ni nakan goge hannayena da shi sa’annan in zo in ci wani abu da hannun, shin ba shi da wata illa idan aka ci?
Amsa: Man goge hannaye wato “Hand Sanitizer” na daya daga cikin hanyoyi biyu na tsabtace hannaye na zamani, wanda hukumomin lafiya na duniya suka tabbatar suna aiki. Na farkon shi ne wanke hannaye da ruwa da sabulu, wanda aka fi so saboda saukin samun ruwa da arahar sabulu. Wadanda ba su samu sabulu ba amma suna da ruwa, hukumomin lafiya suka ce ko toka ce su sa su murtsuka hannun sosai ciki sa’annan su dauraye da ruwa.
Hanya ta biyu ita ce ta amfani da man wanke hannu na sanitizer mai dauke da sinadarin alcohol (amma fa ba ruwan giyan ke nan ba, domin a can baya mun taba bayanin bambancin alcohol da ethanol, wanda shi ne ruwan barasa). Shi wannan sinadari yana kashe kwayoyin cutar da ke hannayenmu ne, maimakon wanke su da ruwa da sabulu kan yi. Wannan hanyar tsabtace hannaye Hukumar Yaki da Cututtuka masu Yaduwa ta Duniya (CDC) ta ce za a iya amfani da ita idan ba a samu ruwa da sabulu ba, kuma idan ba a ganin datti baro-baro a hannayen, domin idan akwai dattin da ido zai iya gani dole ne a samo ruwa da sabulu a wanke, tun da shi ruwan alcohol ba zai wanke datti ba.
To, idan babu dattin da ido zai gani, ana iya amfani da shi ruwan sinadarin alcohol din, kuma bayan an shafa a hannayen ciki da waje, gaba da baya an murtsuka sosai, ana so a yarfe hannayen ne su bushe, ko a sa su karkashin fanka ko na’urar busarwa ko na’urar sanyaya wuri, wato dai a tabbata sun bushe, ko a goge da wani mayani kamar na takarda mai tsabta da akan kira tissue. To in dai suka bushe aka yi amfani da hannun wajen cin abinci babu wata matsala. Don haka ke nan idan aka yi amfani da wannan ruwa, busar da hannayen kawai ake bukata mutum ya yi.
Duk wasu al’adu na bayan cin abinci, kamar na sude hannu kawai ba tare da wankewa bayan an side ba, ko na goge hannu a ka kawai ba tare da wankewa ba idan an ci abinci, a dauka wai hannayen sun fita, duk ba sa cikin tsarin kiwon lafiya.
Wai a ruwan sama ake shan ciwon Typhoid ne?
Daga Maryam Maraba
Amsa: A’a, ba a ruwan sama ba ne, domin idan mutum ya tari ruwan sama kai-tsaye ya sha, ba zai kwashi ciwon Typhoid ba, amma idan ruwan saman ya riga ya taba kasa aka diba aka sha, to ba Typhoid ba, watakila abin da ya fi Typhoid ma ya riga ya hadu da ruwan ba a sani ba. Don haka ba za a sa ruwan sama da ya taba kasa a cikin tsabtattun ruwa ba. Amma kuma wani iko na Allah ruwan da zai bubbugo daga kasa wato daga karkashin kasa da akan kira idon ruwa ko mabubbugar ruwa, za a sa shi cikin tsabtatattun ruwa saboda daga karkashin kasa yake, sai ya kwaranya a kasa ne watakila zai gurbata. Ke nan shi ma ruwan karkashin kasa ba zai sa ciwon Typhoid ba.
Na ji idan kuna maganar rage kiba sai ku ce a rika motsa jiki. To game da masu matsalar nakasa kamar ta kafa wadanda ba za su iya tafiya ko gudu ba yaya za su yi?
Daga Muhammad Babangida, Kaduna
Amsa: A’a, haba Malam Muhammadu, sai ka ce ba dan birni ba? Motsa jiki ai har masu nakasa suna yi. In dai kana kallon talabijin ai babban misalin motsa jikin nakasassu da za ka ilimantu da shi shi ne shirin wasannin nakasassu da akan kira Paralympics, wanda a ciki akan ga yadda nakasassu suke motsa jiki iri-iri ba wai dole sai gudu ko tafiyar sassarfa ba, ga su nan barkatai. Idan ma kana ganin kamar babu irin wadannan wasanni a kasar nan ai za a iya samun ko da irin kwallon Tennis din nan ta teburi ne, ko iyo a ruwa ko dambe ko sukuwar doki, ko tseren keken guragu. Ga su nan dai barkatai wadanda duka ba sa bukatar lafiyar kafafu.
Idan mutum na ciwon ido kamar na Apollo sai ka ji ana cewa ya shafa fitsari a idanun. Ko hakan na da wani tushe?
Daga Maman Umar, Legas
Amsa: A’a, a kimiyyance wannan ba ya da wani tushe. Su cututtukan ido irin na Apollo kwayoyin cutar birus ne suka fi kawo su. Don haka sai an je likita ya gani ya tabbatar hakan ne ya ba da maganin da ya dace.
Na kasance idan zazzabi ya zo mini sai ya zo da ciwon makogwaro mai zafi don ko ruwa ma ba na iya sha. Me ke kawo haka?
Daga Tarasulu, Darmanawa
Amsa: A’a, akasin haka ne matsalar, wato ba zazzabin ba ne ya kawo ciwon makoshin, a’a, ciwon makoshin ne ya kawo zazzabin. Yawanci irin wannan ciwon makoshi mai zafi, kwayoyin cuta na bacteria ke kawo su, domin watakila ma da za a leka makoshin har diwa za a iya gani a kan ’yar wuya. Don haka yana da kyau da irin haka ya fara miki ki je asibiti ko da karamin asibiti ne likita ya leka ya gani ko haka ne, ya rubuta miki magani. Yawanci masu samun irin wannan matsala sukan yawan samun ta duk bayan ’yan watanni, don haka sai sun dauki matakin kariya na gaske kafin su daina samun ciwon, wanda yawan wanke hannaye sau da dama da ruwa da sabulu a kowace rana shi ne kan-gaba.
Duk lokacin da raina ya baci sai na ji numfashina da kyar yake fita, ko me ya sa?
Daga Aminu A. Gumel
Amsa: Ba wani abu da zai dame ka in dai sai lokacin da ranka ya baci abin yake zuwa. Sako ne kawai da kwakwalwarka kan kai hanyoyin numfashinka kan dan samu yankewa idan kana yawan fushi. Don haka sai ka rage yawan fushi.