✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan da ciwon damuwa ke haifarwa

Idan damuwa ta yi wa mutum yawa me take haifarwa? Domin ni shekaruna ba su wuce 18 amma ban san dadin rayuwa ba kwata-kwata kullum…

Idan damuwa ta yi wa mutum yawa me take haifarwa? Domin ni shekaruna ba su wuce 18 amma ban san dadin rayuwa ba kwata-kwata kullum cikin bakin ciki da ciwon kirji kamar wani abu ya tsaya min a wurin. Shi ne nake neman shawara

Daga Yarinya Mai Damuwa

 

Amsa: Tunda za a saya sunanki da lambarki saboda halin aikin likitanci idan ya hada da halin aikin jarida, ba wanda ya san sunanki balle inda kike. Ke kadai ce za ki karanta wannan amsa ki san da ke ake. Da da hali sai a tuntubi magabatanki a yi musu bayani. Amma tsarin aikin bai yarda da haka ba, sai dai shawarar kamar yadda kika nema.

Ciwon damuwa ciwo ne da kan sa yawan dacin rai ko bakin ciki kamar yadda kika fada, wani abu ya zo ya tsaya a kahon zuci kamar dutse a wasu lokutan. Akan yawan samun rashin barci da rashin iya cin abinci da yawan tunani na ba gaira-ba dalili, kai har ma da yawan kuka a wasu lokuta mutum ya rasa abin da ke masa dadi a duniya.

To idan matsalar ta yi yawa ba a yi magani ba har zuciya kan yi sake-sake na cutar da kai, wato mai ciwon ya ji wata zuciyar a jikinsa tana rada masa sai ya cutar da kansa ko ma ya hallaka kansa sa’annan abubuwa za su dawo daidai. Haka nan idan ciwon ya yi kamari akan kuma iya samun rashin iya ci gaba da harkoki na yau da kullum kamar zuwa aiki ko zuwa makaranta har watakila matsalar ta sa a kori mutum saboda fashi. Matsalar kan sa mutum ya yanke zumunci da alaka da ke tsakaninsa da ’yan uwa, tunda ba kowa ba ne zai gane cewa mutum na da ciwon damuwa. Su ma wadannan duka ba karamar asara ba ce ga rayuwar mai matsalar duk suna daga cikin abubuwan da ciwon kan jawo. To duk wadannan illolin da ciwon tunani ke kawowa ke nan idan ba a yi maza an tare shi ba.

Shawara dai, tunda ba ganinki aka yi ido da ido ba, ita ce ki daure ki fada wa iyayenki ko wani babba na kusa wanda kike ganin zai fahimce ki domin su daure su kai ki asibiti a duba lafiyarki a gani ko ciwon damuwar ne ko wani abu daban.

 

Ina fama da wata matsala ce da ta dade tana ci min rai. Ni dai kasa nake ci kusan shekara biyar ke nan na kasa bari, shi ne na ke neman shawara

Daga Mai Cin Kasa

 

Amsa: Eh, tabbas wannan matsala ce ko a likitance. Ciye-ciyen abubuwan da ba a ci a al’adance matsala ce da a likitance muke alakantawa da abubuwa biyu zuwa uku, ko dai matsalar karancin jini ko kuma matsalar tunani.

 

Ni kuma idan ina kuka ne sai in ji kamar in fadi. Ko hakan matsala ce?

Daga Asma Yashe

 

Amsa: A’a in dai ba kukan ne ya fiya yawa ba, ba wata matsala ba ce.

 

Ni kuma idan hannuna ya hadu da karfe ne nake ganin tartsatsin wuta kamar shocking. Ko akwai matsala ne a jikina?

Daga Bilya M. Sakaba

 

Amsa: A’a ba wata matsala in dai ba wutar gasken ka taba ba. Bambancin halitta ne kan sa wadansu kullum hannayensu akwai cajin maganadisun da idan ya hadu da wani abu kamar karfe ko ma hannun wani mai akasin cajinka sai dan tartsatsi ya tashi wanda ba ya cutarwa.Amma a lantarki da yake yana da karfi shi zai iya cutar da zuciya, daidai karfin abin da aka taba.

 

Na kan ji ciwon cibi har tashi ya yi min wahala. Amma yakan saki nan da nan kuma sai in ji kamar ba ni ba. Ko shin haka matsala ce?

Daga Aminu A.

 

Amsa: Eh, kwarai matsala ce a cikinka ko a hanji ko a karshen hanji wanda muke kira appendid. Don haka sai ka je an duba an gani. Idan ba ka je an duba an yi magani ba, a likitance ana ganin abin zai zo ya fi haka ta’azzara

 

Ni kuma idan na ci abinci bayan wani lokaci sai in ji wani tsinkakken yawu mai kanwa-kanwa ya biyo makoshina, can sai amai da gyatsa. Me ke kawo wannan?

Daga Idris B.G

 

Amsa: Da alamu ruwan sinadarin acid na ciki ne ke tasowa. Ko dai yana yi maka yawa idan ka ci abinci ko kuma akwai gyambo a cikin, wato olsa. Don haka ka samu ka je ka ga likita ya tantance ya kuma ba ka magani.

 

Tambaya ce da ni game da tsarin lafiya na adashin gata. Idan na yi rajista da kamfanonin HMO a wani asibiti zan iya zuwa wani asibitin daban da rijistar?

Daga Bashir Muhammad Ikko

 

Amsa: Wannan tambaya Malam Bashir ai su kamfanonin za ka yi wa. Tunda mun fada a bayanin baya cewa su kamfanonin za su gaya maka asibitocin da suke da yarjejeniya da su, wadanda za ka iya zuwa.

 

Ina fama da matsanancin sanko kuma shekaruna 26 ne. Shi ne nake tambaya ko akwai maganinsa? A ina za a samu?

Daga Abdullahi Aliyu

 

Amsa: Eh, kwarai wasu nau’o’in suna da magani, wasu nau’o’in kuma ba su da shi. Za ka iya samun maganin idan ka je likitan fata ya duba ya ga kowane iri ne, sai ya rubuta maka ka gwada ko za a dace