✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abu 5 da ke sa masoya batawa a lokacin hira

Duk mai yin wadannan abubuwan to ajalin soyayyarsa ya kusa

A yayin da masoya ke son yin hira da juna, sau tari a lokacin haduwar ne ake samun bacin rai da ke kaiwa ga rabuwa saboda yadda suke bata rawarsu da tsalle.

Aminiya ta zatan da wasu maza da mata inda suka bayyana abubuwan da ke kawo hakan da ma wadanda ba sa kauna masoyansu su yi a lokacin hira a tsakaninsu.

Ga biyar daga cikinsu da masoyan da muka zanta da su suka ce suna iya kawo karar kwanan soyayya:

Dogon jira

Galibin masoya ba sa son dogon jira idan suka je hira ko za a zo musu hira, musamman idan a lokacin suna son gabatar da bakinsu ga masoyansu.

Wani lokaci tun kafin masoyan su yi ido hudu da juna bacin rai ke bayyana daga wanda aka bari yana dogon jiran.

A zantawar Aminiya da Abbah Ibrahim, ya ce yawancin maza sun tsani dogon jira idan suka je zance wajen budurwa.

“Wannan dadewar na kona masa zuciya koda a cikin farin ciki ya zo, domin wasu mazan na ganin hakan wulakanci ne.

“Wata budurwar ta san zai zo, maimakon ta shirya da wuri sai ta bari sai ya iso za ta fara shiryawa, wata ma a lokacin za ta shiga wanka.

“Sai ya gama bata lokacinsa idan yana da wani uzirin sai dai ya hakura tunda ta riga ta bata masa lokaci da sauran abubuwan da ya tsara a ranar.”

Wasu matan na ganin cinyewa ne su bar namiji yana jira, wasu kuma rashin tsari ne da su wanda hakan kan sa mazan yi musu ba daidai ba har ta kai ga su mazan ake dogon jira.

Amma yana da kyau su fahimci cewa masoyansu sun zo ne da alheri kuma sun cancanci mutuntawa.

Ciye-ciye

Duk da cewa ana ganin wayewa ce ko alamar sakin jiki da juna cin abu a wurin saurayi ko budurwa, wasu kuma na ganin hakan rashin kamun kai ne.

Wasu mazan sun tsani mace ta fito hira wurinsu tana taune-taune ko a lokacin da suke tare.

Sadeeq Muhammad ya ce, “wata macen kan fito zance tana taunar cingam kuma maza da yawa sun tsani hakan, idan wani na son hakan to wani ba ya so, a nawa tunanin ma babu wanda zai so hakan.”

Rashin magana

Aliyu Rabiu ya ce, “maza ba sa son su je zance kuna hira ki yi ta ce masa ‘uhmm’ ko kuma ‘ina ji’, shi ma hakan maza da yawa basa so.

“Shi namiji yana so ki bude baki ki yi masa magana kar ki ce ‘ai yin hakan zubar da aji ne’ —akwai abun da yin su ba zub da aji ba ne.”

Maimaita zance

Duk da cewa mace na son ganin saurayi ya zo wurinta sun yi hira, akwai abun da ke gundurar, saboda haka a rika canja salon hirar.

Wasu matan ba sa son wanda kullum sai ya zo hira da mai yawan maimaita magana daya kullum.

Da take bayyana mana cewa ba ta son saurayi mai maimaita magana daya kullum, Sadiya Abubakar ta ce mene ne amfanin “ka zo zance amma hirar da za ka yi mata ta wancan zuwan da ka yi ne?

“Yana da kyau kafin ka je zance ka tsara abin da za ka fada mata ya sa ta farin ciki, idan ka tafi ta rika tuna ka har ta yi mafarkin ka.”

Sakin layi

Kar ka je hira kama yi wa mace hirar abin da ba ta so ko bai shafe ta ba, musamman hirar kwallon kafa.

Wasu daga cikin ’yan matan da muka tattauna da su sun bayyana cewa, “duk saurayin da ke yi wa mace hirar kwallo, to za ta tsani hirar, a wani lokaci har shi saurayin.”

Saboda haka, duk da cewa wasu matan su ma ’yan kwallon ne, to amma dai da yawan mata ba sa bukatar irin wannan hirar, kuma ai ba abin da ke tsakaninku ba ke nan.