✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa zan gina jami’ar Musulunci a Daura – Rochas Okorocha

Ya ce hakan sakayya ne kan irin alheran da Buhari yake wa Najeriya.

Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Sanata Rochas Okoracha ya yi alkawarin gina Jami’ar Musulunci a garin Daura, mahaifar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ke Jihar Katsina.

Ya ce zai yi hakan ne saboda matukar kaunar da aka nuna masa a masarautar da ma Jihar Katsina baki daya.

Rochas, wanda jigo ne a jam’iyyar APC mai mulki ya ce gidauniyarsa ta Rochas Foundation ce za ta dauki nauyi da dukkan dawainiyar jami’ar.

Ya kuma ce gidauniyar tasa ta gina makarantu da dama tare da aiwatar da ayyukan raya kasa a jihohi da dama, inda ya ce yin wannan aikin a Daura kamar sakayya ne ga irin alhairan da Shugaba Buhari yake yi wa Najeriya.

A kwanan nan ne dai Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar ya nada Rochas din sarautar Maga Alherin Kasar Hausa.

A yayin wani taro da ya gudana a garin na Daura a karshen mako, tsohon Gwamnan ya ce jami’ar za ta kasance kyauta ce kuma har da dakunan kwanan dalibai za a gina a cikinta.

“Saboda Sarkin Daura ya bani mukami a masarautarsa, zan yi wata kyauta wacce watakila ba za a taba mancewa da ita ba.

“Zan gina Jami’ar Muslunci da dukkan kayan alatun zamani karkashin gidauniyar Rochas Foundation a garin Daura, kuma ni da kaina zan zo in kaddamar da ita,” inji shi.

A baya dai, Gwamnatin Tarayya ta sanar da kudurinta na gina Jami’ar Sufuri a garin na Daura da hadin gwiwar wasu ’yan kwangila na kasar China da suke yi wa gwamnati aikace-aikace.