✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da muke yi don inganta ayyukan fannin tarho – dambatta

A cikin wannan tattaunawa da jaridar Daily Trust, Babban Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) Farfesa Umar Garba dambatta ya bayyana abin da hukumarsa…

A cikin wannan tattaunawa da jaridar Daily Trust, Babban Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) Farfesa Umar Garba dambatta ya bayyana abin da hukumarsa ke yi wajen inganta harkokin tarho a kasar nan.

 

Hukumar NCC ta gana da dukan masu gudanar da harkokin tarho; me ya faru?

Dukkan masu gudanar da harkokin tarho suna nan ne domin mun gano an samu tabarbarewar ingancin ayyukansu. A baya masu amfani da tarho ne suke korafi kan ingancin ayyukan kamfanonin, kuma korafin ba lallai ne ya zama gaskiya ba. To amma ka san a karon farko an samu ittifaki a tsakanin abin da masu amfani da tarho suke fadi na rashin ingancin ayyukan da kuma ma’aunan da muka yi amfani da su wajen gwaje-gwaje a kimiyyance, wadanda a karshe suka nuna tabarbarewar ingancin ayyukan kamfanonin.

 Don haka a shirye muke mu nuna wa masu kamfanonin tarho din wadannan hujjoji. Domin a matsayina na masanin kimiyya kuma injiniyar da ya samu horo, ba za ka ce ingancin aiki ya fadi kasa ba, sai ka kawo hujja da shaidar da za su tabbatar da wancan bayani.

To, mun gabatar da bayanan da suka kamata ga dukan masu kamfanonin ciki har da dukan na’urorin da suke rarraba ayyukansu. Don haka za su iya ganin ma’aunan ayyukan da suka gudanar (KPIs) da muka auna su jiha bayan jiha kuma aka fadada su domin nuna matakin da masu amfani da tarho suke ciki a matakin kasa. Wannan lamari ne da ba a taba yi ba a baya. Wadannan ma’aunan ayyuka (KPIs), musamman sun shafi koma-bayan da aka samu kan kudin kiran waya. Kuma wannan muhimmin ma’auni ne, domin an ce a cikin kira 100, daya ne kawai ya kamata ya gaza. Don haka a ka’ida kashi 1 cikin 100 ke nan. Kuma mun iske kusan galibin masu kamfanonin tarho din bas u cimma wannan ka’ida ba a wurare da dama, musamma a Legas da Abuja da jihohi da daman a Kudu maso Yamma da Kudu maso Kudu a watannin Oktoba da Nuwamba da Disamban 2016. Muna da dalla-dallar bayanai na watannin uku. Don haka babbar manufar ita ce masu kamfanonin tarho su gani da idonsu, domin wadannan bayanai an cirato su ne daga bayanan da masu kamfanonin suka gabatar ga Hukumar NCC, wadanda muka daddale su kuma muka yanke shawarar cewa ma’aunan ayyuka KPI kana bin da ya shafi gazawar kira ba a cin musu ba.

Kuma a karshe manyan masu kamfanonin sun amince, amma sai suka ce suna fuskantar matsaloli ne kuma suka bayyana matsalolin da:  

Katsewar wayoyi da batun da ya shafi al’ummu da kuma hakkin mallakar hanya (RoW) da haraji iri-iri da batun samun kudin musaya da sace kayayyakinsu da barayi ke yi da rurrufe tashoshin isar da sakonni barkatai da sauransu. Sun ce wadannan duka suna hana su samun kayayyakin da suka kamata domin inganta ayyukansu a abin da ya shafi kaiwa ga abokan cinikinsu. 

Kuma mun yi musu bayanin dukan kokarin da muke yi don taimaka musu su warware wasu daga cikin wadannan matsaloli, kuma muka bukaci su kara inganta ayyukansu. Hasali ma mun ja musu kunne cewa: Ingancin ayyukansu a yanzu ba abin lamunta ba ne, ya alla ga abokan ciniki ko ga Hukumar NCC wadda babban aikinta shi ne ta kare tare da karfafa masu amfani da tarho.

Wannan ya zo daidai da batu na shida na kudirori 8. Kuma kudiri na biyu na wadannan kudirori shi ne na inganta ayyukan kamfanonin tarho. Domin haka ba mu yi wani abu da ke wajen abin da muka ce za mu yi ba, lokacin gabatar da wadannan kudirori a shekarar 2016. Don haka muna ci gaba da gudanar kudirorinmu ba mun tsaya kan karatun zuku ba ne. Lokacin surutu ya wuce. Muna aiwatar da kudirorinmu a yanzu wadanda suka shafi karewa da karfafa gwiwar abokan ciniki.

Ka hango samun sauyi mai amfani wajen ingancin ayyukan a nan kusa?

Eh, za mu ci gaba da sanya ido kan ingancin aikin. Wadancan ma’aunan ayyuka da aka sanya (KPIs) za a sake amfani da su. Mafi muhimmanci dai adadin rashin samun layi ya ragu; wannan shi ne abin da ya fi damun ’yan Najeriya. Yanzu haka muna yin na watannin Janairu da Fabrairu da Maris. Kuma za mu jira zuwa lokacin da sashin  sanya ido da kididdiga ya kammala nazarin Data na farkon rubu’in shekarar 2017. A lokacin da suka kammala suka yin nazari za mu gwada su da na rubu’in karshen shekarar 2016 don mu ga ko an samu inganci ko an dada tabarbarewa. Ba zan ce komai ba a yanzu har sai an kammala nazarin. Amma mun san abin da za mu yi bayan an kammala.  

Wannan tattaunawa an buga ta a karon farko a jaridar Daily Trust on Sunday a shekarar 2017