✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba Kyari ya fara farautar wadanda suka kai wa Ortom hari

Rundunar ta hado kwararrun masu binciken kwakwaf da gano zanen yatsu

Dan sanda mai farautar ’yan fashi da masu satar mutane, DCP Abba Kyari da dakarunsa sun isa Binuwai domin kamo ’yan bindigar suka kai wa Gwamna Samuel Ortom na Jihar farmaki.

Rundunar ta Abba Kyari ta isa Makurdi ne bisa umarnin Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu, na yin cikakken bincike tare da kamowa da kuma tabbatar da hukunta masu alaka da harin.

Kakakin ’Yan Sanda na Kasa, Frank Mba ya ce, “Za ta jagoranci bincike kan harin daga kowace fuska da aka bayar da rahoto da zummar tabbatar da cafko duk wadanda dalilai suka nuna suna da hannu da kuma gurfanar da su.”

Rundunar da Abba Kyari ke jagoranta ta kunshi kwararrun masu binciken kwakwaf kan inda aka aikata laifi, ababen fashewa, gano zanen yatsu, da sauransu.

Frank Mba ya ce, “Shugaban ’Yan Sandan Najeriya ya umarce su da su su nuna kwarewa a yayin gudanar da aikin tare da hadin gwiwar Rundunar ’Yan Sandan Jihar Binuwai da sauran hukumomin tsaro domin cimma manunfar binciken.”

Gwamna Ortom ya ba da rahoto cewa ’yan bindiga sun kai masa farmaki a Tyomu, yayin da yake hanyarsa ta dawowa Makurdi daga gonarsa a babbar hanyar Makurdi zuwa Gboko.

Wasu ’yan Najeriya sun bayyana tababarsu game harin, amma gwamnan ya ce ba yadda za a yi ya shirya kai masa hari domin a cikin masu tsaronsa akwai Hausawa da Fulani da Yarbawa.

Shugaba Buhari dai, yayin karbar bakuncin Ortom a makon jiya ya yi tir da harin sannan ya yi gargadi cewa a yi hattara da neman siyasantar da al’amarin.