✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A yi sata, a yi kisa, a yi rashin kunya sai Najeriya! (2)

Ana sane da Dala biliyan 20 na mai da aka sace, amma babu abin da suka yi a kai

Da aka kafa Kwamitin Faruk M. Lawal a kan almundahanar Naira tiriliyan 2.7 na tallafin man fetur, sai ga Faruk Lawan din ya zaga ya karbi Dala dubu 600, maganar ta lalace ba a ko dakatar da shi ba, amma aka dakatar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya da ya bankado satar Dala biliyan 49.8, ya ki karbar hanci.

Haka Obasanjo ya aikata laifuffukan tsigewa har 125, maimakon a tsige shi, sai shi ne ya rika tsige shugabannin majalisa. Sai da talakawa suka yi musu taron dangi muka hana shi zarcewa.

Haka kuma duk ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa sai yadda aka yi da su. Suna sane da Dala biliyan 20 na mai da aka sace, amma babu abin da suka yi a kai.

Haka al’amura suke ta ci gaba da lalacewa saboda an riga an raba akasarin mutane da tsoron Allah an cusa musu son dukiya.

Babu babba babu yaro ba mace ba namiji ba talaka ba sarki, kowa kawai burinsa ya tara kudi kamar Karuna.

A takaice dai tsarin da Janar Ibrahim Babangida ya dora kasar nan a kai shi ne tushen rusa tarbiyya da tsoron Allah a zukatan akasarin ’yan Najeriya.

Shi kuma Cif Olusegun Obasanjo ya zo ya mayar da Janar Babangidan dakiki, bagware! Sai yadda Obasanjo ya yi da su Babangida da kowane Gwamna da ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa, shi ya sa ya yi ta cin karensa babu babbaka, ya mallake PDP ya kwace ta daga wadanda suka kafa ta.

Tsare-tsaren IBB ne suka rusa tsarin aikin dan sanda da kotu tare da dora tattalin arzikin Najeriya a kan gadar rushewa, shi ne shugaban da ya fara mallaka wa kansa da abokansa rijiyoyin man fetur.

Shi ne Shugaban da ya lalata siyasar akida da kawo ci gaba.

Ya rika shirya zabe yana sokewa yana halattawa da haramta wa ’yan siyasa damar tsayawa takara.

Hakan ne masomin tazarce a Najeriya, domin ya shirya zabe ya soke duk tazarce ce a kaikaici, shi ya sa a karshe da ya soke zaben 12 ga Yunin 1993, ya nemi ya zarce.

Kuma hakan ne ya sa su Janar Sani Abacha da Olusegun Obasanjo suma suka jarraba zarcewa.

Duk irin wadannan su ne suka haifar da halin da ake ciki a yanzu.

Ya rage ga dukkan wadanda abin ya fi shafa su tuna yadda muka hana Babangida ya zarce da yadda aka hana Obasanjo ya canja kundin Tsarin Mulkin Najeriya don ya zarce.

Mece ce mafita?

Ga fahimtata gyara ba zai yiwu a sauki ba, idan har ana son a sake mayar da Najeriya kan turbar kwarai dole ne a dauki matakan da suka hada da hukunta dukkan mutanen da suka aikata kowane irin laifi, kamar yadda ake yi a kasashen duniya.

Wajibi ne hukunta manyan shugabanni kamar yadda ake hukunta kowa a bainar jama’a.

Kuma ya kamata kowa ya fara jingine duk wani burinsa na a zabe shi a kowane mukami, sai an tabbatar da cikakkiyar doka da oda, duk wadansu da ake zargi da aikata laifuffuka an hukunta su, koda ya zama tilas a yi gwamnatin rikon kwarya ce a karkashin Babban Jojin Najeriya.

Kuma a gurfanar da dukkan wadanda ake zargi da laifi a gaban kotun hukunta shugabanni da duk masu aikata manyan laifuffuka ta duniya.

Har yanzu tsarin mulki na soja ake amfani da shi tun lokacin mulkin Obasanjo na soja har zuwa Sani Abacha da Abdulsalami Abubakar zuwa yanzu.

Shi ya sa nake ta yin kira ga ma’abota hankalin cikinmu, masu ra’ayin siyasa da dimokuradiyya ta gaskiya, kowa ya jajirce sai an kafa gwamnatin rikon kwarya mai wakilcin zallar farar hula da ba su da tabo na kowane laifi, ko mummunan zargi a kotu a karkashin shugabancin Babban Jojin Najeriya.

Kowace jiha ta bayar da wakilai daidai da yawan mutanenta, idan tana da mutum miliyan 10 ta bayar da wakilai 10, mai miliyan biyar ta bayar da wakilai biyar, mai miliyan uku ta ba da wakilai uku, wato duk mutum miliyan daya wakili daya mutumin kirki.

Su ne za su bi kadin dukkan abubuwan da suka faru tun daga lokacin Obasanjo na soja, su dubi duk zaluncin da aka yi wa talakawa na sata da kisa da sauransu, a kwato wa kowa hakkinsa, masu laifi a hukunta su.

Sannan a kafa kwamitin sabon tsarin mulkin Najeriya na farar hula zalla, sannan a kafa sababbin jam’iyyun siyasa da hukumar zabe, a tsara jadawalin zabe.

Wannan ne abin da ya wajaba a yi koda zai dauki tsawon shekara biyu ko fiye.

Yin haka ya fi alheri a kan a ci gaba da wannan gurguwar tafiyar siyasa marar alkibla ta neman tara abin duniya ta halal da haram da kwace da danniya, wanda hakan ne silar yawaitar barayin daji masu garkuwa da mutane, suna kwace dukiyarsu suna kashe su.

Matasan da ba ku riski lokacin da abubuwan da na yi bayani a kansu ba sai ku yi bincike a ma’ajiyar littattafai da jaridu da mujallu (library) ku kara wa kanku ilimi.

Wadanda kuma suka manta su tuna. In dai wadannan masifun da suka addabi Najeriya a yanzu ba su isa su zama sanadin haduwar kan mutanen kirki a kasar nan su dauki matakin yin gyara ba, to, za mu dade muna kuka.

Tilas mu kawar da matsorata da munafukai da makwadaita, wadanda ba ruwansu da Allah sai kudi, ba sa son ’yanci sai NAIRA.

Mu tuna dole za su mutu, kuma mutum bai isa ya zabi lokacin da zai mutu ba, ko irin mutuwar da zai yi, ko wurin da ya fi so ya mutu, ko shi wane ne ko dan wane ne!

Ana iya duba jaridar Aminiya ta ranar Juma’a 18 ga Yulin 2014 da ta ranar Juma’a 18 ga Afrilun 2014, shafi na 11, domin ganin wasu bayanan.

Alhaji Abdulkarim Daiyabu shi ne Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN) za a iya samunsa ta: 08060116666,08023106666, 09094744184