Ana gwaje-gwaje kafin daura aure a masallatai kan ciwon qanjamu me ya sa aka tsaya a iya na qanjamau?
Wadannan gwaje-gwaje da ake yi zamani ne ya kawo, domin tabbatar da lafiyar ma’aurata saboda gudun yin aure wani yana da ciwon (da zai harbi dan uwansa). Mun fi mayar da hankali ne kan gwajin qanjamau saboda shi ne aka fi ganin yana halaka mutum a zahiri amma yanzu ka farkar da mu za mu yi kira a sanya sauran gwaje-gwajen a cikin tsarin.
Ta yaya za ku jawo hankalin al’umma domin ganin ana yin sauran gwaje-gwajen?
Zan yi magana ga sauran malamanmu a wajen ganawa in gaya musu muhimmancin yin gwajin sikila da na hanta wadanda su ma cututtuka ne masu illa da akan gaje su. Idan suka amince sai mu fadakar da jama’a ta hanyoyin huduba a masallatai da wuraren wa’azi domin gaskiya da ba mu cika damuwa da wadannan gwaje-gwajen ba, idan muka ga na qanjamau din ya wadatar sai dai muna ba da shawarar yin na sikila din, amma yanzu za mu sa a hada duka.
Kamar na ciki kun tsananta a kai ke nan shi ma ko dai ba a cika damuwa da shi ba?
A’a mun tsananta a kai domin gudun kada a yi aure da ciki domin kana iya ganin mace a ido saliha amma idan aka bincika sai ka ga an samu akasin haka, wanda ba za a iya ganewa ba sai ta hanyar yin gwaji.
Yanzu ana iya daura aure a masallatanku ko babu takardar gwaji?
Gaskiya a wasu masallatan da muke da su ba yadda za a yi a daura maka aure ba tare da ka kawo takardar gwaji kowace iri ba.
Mene ne saqonka ga sauran sassan da ba sa qarfafa yin gwaji kafin aure?
Saqona shi ne a mayar da yin wannan gwaje-gwajen ya zama doka saboda rashin yin wannan gwaji yana iya zama hadari ga rayuwa domin wani zai iya cutar da wani ta hanyar sanya masa cutar idan ba a yi gwaji ba, amma ta hanyar gwaji za a tabbatar da lafiyar kowane bangare.
Kuma muna godiya ga kafafen watsa labarai musamman jaridar Aminiya kan yadda take qoqarin wayar da kan jama’a ta hanyoyi daban-daban.