✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A kori Secondus daga PDP kafin ya rusa ta —Matasa

Kiran na zuwa ne bayan yawan sauya shekar mambobin jam'iyyar.

Matasan Jam’iyyar PDP sun yi kira da babbar murya da a kori Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Prince Uche Secondus daga cikinta.

Wannan na zuwa ne bayan sauya sheka da wasu ’ya’yan jam’iyyar suka yi a watannin da suka gabata.

  1. Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya lalace a daji
  2. Matar Ganduje na son a rika yi wa ma’aikatan Kano gwajin miyagun kwayoyi

A makonnin ne Gwamnan Jihar Kurso Riba, Ben Ayade da Sanata Peter Nwaoboshi suka sauya sheka daga jam’iyyar zuwa APC.

Kazalika, rahotanni sun bayyana cewar Gwamnan Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya shirya tsaf don barin PDP zuwa APC.

Matasan jam’iyyar ta PDP daga shiyyar Kudu maso Kudu, cikin wani jawabi da Shugabansu, James Efe Akpofure, ya sanya wa hannu, sun bukaci jami’iyyar ta kawo karshen sauya sheka da ake yi daga jam’iyyar.

Shugaban matasan, ya ce za a iya wayar gari babu kowa a cikin jam’iyyar kafin wa’adin Secondus ya cika a watan Disamba.

Akpofure ya ce yawan ficewar da mambobin jam’iyyar ke yi zuwa APC na da nasaba da rashin iya kamun ludayin Kwamitin Gudanarwar jam’iyyar ta Kasa (NWC) da Secondus ke jagoranta.