✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A karshe Amurka ta yi gwajin makami mai gudun walkiya

Ma’aikatar Tsaron Amurka ta ce ta gudanar da gwajin makami mai linzami mai gudun walkiya a cikin nasara.

Ma’aikatar Tsaron Amurka ta sanar da cewa ta gudanar da gwajin makami mai linzami mai gudun walkiya a cikin nasara.

Amurka ta sanar da gwajin makamin ne a ranar Laraba bayan tuni kasashen Rasha da China sun yi gaba a fannin kera makamai masu gudun walkiya.

Nasarar gwajin makamin da cibiyar binciken tsaron Amurka ta yi na makamin da kamfanin kera makamai na Lockheed Martin ya kera na zuwa ne mako biyu bayan rashin nasarar wani gwajin.

Duk da haka ana ganin makamai masu gudun walkiya da Rasha da China suka mallaka babu kamarsu a duniya.

Amurka wadda ke zaman doya da manja da kasashen Rasha da China dai ta shiga damuwa ganin yadda kishiyoyin nata suka shige mata gaba a bangaren mallakar makamai masu gudun walkiya.