✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Tinubu zai yi amfani da damar wajen bayyana wa 'yan Najeriya irin aikin da gwamnatinsa ke yi.

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shirya tattaunawa kai-tsaye da ’yan Najeriya a karon farko, tun bayan hawansa mulki a daren ranar Litinin.

Tinubu, zai tattauna da ’yan ƙasar ne da misalin ƙarfe 9 na daren ranar Litinin, 23 ga watan Disamba, 2024.

Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Watsa Labarai, Bayo Onanuga ne, ya sanar da hakan.

Ya kuma ce za a watsa tattaunawar a gidan talabijin na NTA da gidan rediyon FRCN.

Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan manufofi da nasarori da gwamnatin Tinubu a nan gaba.

Ana sa ran wannan tattaunawar za ta bai wa ’yan Najeriya damar fahimtar irin ƙalubale da da gwamnatin Tinubu ke fuskanta.

Haka kuma, za ta zama wata babbar kafa da za a iya samun ƙarin haske kan shirye-shiryen gwamnatin don farfaɗo da tattalin arziƙi da inganta rayuwar al’umma.

Shugaba Tinubu, na fatan amfani da wannan dama wajen tabbatar wa da ’yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tuƙuru wajen samar da ayyukan yi, tsaro, da kuma inganta ilimi da kiwon lafiya.

Masu sharhi na siyasa, sun bayyana wannan tattaunawar a matsayin wata muhimmiyar hanya da za ta bai wa shugaban damar nuna jajircewarsa wajen cika almawuran da ya dauka yayin yaƙin neman zaɓe.

Wannan tattaunawar za ta kuma bai wa al’umma damar ji kai-tsaye daga bakin shugaban kan irin nasarorin da ya cimma tun daga lokacin da ya hau mulki.