✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A karon farko mata sun yi aikin Hajji ba muharrami

Yadda mata suka yi aikin Hajji ba tare da muharrami ba a karon farko.

Mata sun gudanar da aikin Hajji ba tare da rakiyar muharrami ko wani namiji ba a karon farko a bana.

Ma’aikatar Aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta amince mata masu kowane irin shekaru su gudanar da aikin Hajji ba tare da muharrami ba, da sharadin za su tafi cikin rukuni.

Daya daga cikin alhazan bana marasa muharrami, Bushra Ali Shah mai shekara 35 ’yar kasar Pakistan, ta ce hakan ya ba ta damar cika burinta na tsawon shekaru a Kasa Mai Tsarki.

“Hakan ya cika mini burina! Tun ina ’yar karama ba ni da burin da ya fi na je aikin hajji,” a cewar Bushra, lokacin da take barin gidanta da ke birnin Jiddah zuwa masaukin alhazai.

Ta ce, “Mata da yawa ke yin aikin Hajji tare da ni. Ina alfahari cewa mun zama masu cin gashin kanmu, ba mu bukatar mai kula da mu.”

Hukumomin Saudiyya sun ce kashi 40 cikin 100 na mahajjata 60,000 da ke sauke farali a bana mata ne.

A cewar hajiyar wadda kuma matar aure ce, yin aikin Hajji tare da mijinta ko danta ba zai dauke hankali ta kasa “mayar da hankalinta kacokan a kan ayyukan ibada”.

Mijinta, Ali Murtada, ya ce ya karfafa mata gwiwa da ta yi tafiyar ita kadai, bayan shawarar da gwamnati ta yanke na hana yara shiga aikin Hajji a bana.

“Mun yanke shawarar cewa dayanmu ya tafi. Watakila zuwa badi tana da ciki ko kuma ba za a kara bari yara su shiga ba,” inji mijin nata wanda ke kula da dansu a yayin da take aikin Hajji.

Saudiyya ta takaita halartar aikin Hajjin bana ga mutum 60,000 — masu shekaru 18 zuwa 65, marasa wata cuta mai tsanani wadanda kuma suka kammala daukar allurar rigakafin COVID-19 — da nufin kauce wa cutar COVID-19 wadda ta shekara biyu ana fama da ita.

Aikin Hajji ne daya daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar, kuma ana so duk Musulmi mai iko ya yi shi akalla sau daya a rayuwarsa.

Wasu alhazai mata sanye da takunkumi suna daukar hoto a Filin Arafah a ranar tsayuwar Arafa. (Hoto: Haramain Sharifain).

Barin mata su yi aikin Hajji babu muharrami na daga cikin sauye-sauyen da Yarima Mai Jiran Gado, Mohammed bin Salman ya kawo da nufin zamantar da Masarautar da habaka tattalin arzikin kasar mai arzikin mai.

Bayan hawansa mulki ne aka bai wa mata damar tuka mota da yin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje ba tare da wani waliyi na miji ba —duk da cewa yana shan suka daga ’yan adawa da masu rajin kare hakkin mata.

– ‘Kyautar Allah’ –

Babu tabbas game da lokacin da Ma’aikatar za ta dage wannan takunkumin, amma wasu mata sun yi korafi cewa wasu kamfanonin tafiye-tafiye ba sa son ba wa mata izinin yin tafiya ba tare da namiji ba.

Wasu kamfanoin ma sun soke tafiyar mata a cikin rukuni na tare da muharrami ba.

Ana ganin hakan wata alama ce ta kawo cikas ga sauye-sauyen  da Yarima Mohammed bin Salman ya kawo masu cike da ke rudani a Masarautar.

A baya hukumomi shardanta wa duk wata mata da ke kasa da shekara 45 samun rakiyar muharrami, wanda hakan ya hana mata Musulmi da yawa yin aikin Hajjin.

Irin hakan ya sha ritsawa da Hajiya Marwa Shaker, ’yar kasar Masar da ke zaune a Riyadh, babban birnin Saudiyya.

“Hajji ba tare da muharrami ba wata baiwa ce,” inji ta bayan ta samu damar gudanar da aikin Hajji ba tare da muharrami ba a bana.

Marwa wadda a yanzu take aikin Hajji tare da wasu kawayenta uku, ta ce ta sha kokarin yin aikin Hajji a baya kafin bullar cutar COVID-19 amma ba ta samu saboda ba a ba wa mijinta izinin tafiya.

Bayan samun damar yin aikin Hajjin ba tare da muharrami ba a bana, Marwa mai ’ya’ya uku ta ce, “Ina matukar farin ciki. Allah Ya kira ni duk da matsalolin da ake fuskanta,” inji ta.

Wata likita, Ga Sadaf Ghafoor, mai shaidar kasashen Burtaniya da Pakistan, ta ce yin aikin Hajji ba ba tare da muharrami ba shi ne “hanya daya tilo” da take da shi.

“Ba zai yiwu mu bar ’ya’yanmu a gida ba su kadai,” inji likitar mai shekara 40.

Mijinta ya zabi ya zauna a gida ita kuma Ghafoor ta je ta yi aikin Hajji tare da makwabtansu.

Ta ce, “Ba abu mai sauki ba ne mu dauki shawarar mu … amma mun dauki wannan damar a matsayin alheri.”