✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaki ya tsere ya shiga cikin unguwa

Ana neman zakin bayan ya tsere daga gidan mai shi ya shiga cikin unguwa.

’Yan sanda sun gargadi mazauna da su zauna cikin ankara bayan wani zaki ya tsere daga inda ake tsare da shi.

’Yan sandan birnin Dubai sun yi wa yankin da ke makwabtaka da birnin kawanya domin gano dabbar mai hadari.

’Yan sanda sun bukaci jama’a su sanar da su kawo rahoto a duk inda suka ga dabbar, sai dai ba su magen dajin da ta kwace ba, amma ofishin yada labarai na gwamnatin Dubai ya ce daga cikin dangin zaki ne.

“’Yan sandan Dubai din sun ce kawo duk wata dabbar dawa a bainar jama’a ya haramta a karakshin dokokin kasar; Duk wanda aka kama da yi wa dokar karan tsaye zai sha dauri har na wata shida tare da tara mai girman gaske,” kamar yadda ofishin yada labaran ya nuna.

Dabi’ar ajiye zakoki da damisoshi da dangoginsu a matsayin dabbobin gida ba bakon abu ba ne a wasu biranen kasashen Larabawa, musamman Dubai inda ake ganin hakan a matsayin wani abin nuna kasaitakar arziki da iko.

Duk da yake ajiye dabbobin dawa masu hadari a gida ya saba doka a kasar Hadaddiyar Daular Larabawan; an sha ganin mutanen kasar na yawo da zakokin a cikin motocin alfarma yayin tafiye-tafiyensu.

Wani zaki ya tsere daga wani gida a yankin Al Barsha mai makwabtaka da birnin Dubai a 2016 kafin daga bisani ’yan sanda su kama shi.

A kasar Kuwait, an gurfanar da wani mutum a 2014 bayan zakin da yake gidansa ya kubuce masa inda ya far wa wata budurwa ’yar Filipins.