Gwamnatin Kasar Amurka ta ce za ta mara wa Najeriya baya dangane da zaben 2023 don tabbatar da masu kada kuri’a sun samu aminci a yayin zaben.
Amurka ta bayyana hakan ne ta bakin ofishin jakadancinta a Najeriya.
- Mun kama bako da kullin hodar iblis 105 daga Brazil —NDLEA
- 2023: Peter Obi ne dan takarata —Obansajo
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito Amurka za ta mara wa kasar baya ne karkashin shirin ‘Vote023’.
Vote023 shiri ne na musamman don wayar da kan jama’a kan harkokin zabe musamman ganin yadda zaben 2023 ya karato.
Daya daga cikin jagororin shirin ‘Vote023’, Misis Angela Ochu-Baiye ce ta bayyana haka ranar Asabar a Legas.
Ochu-Baiye ta ce abin a yaba ne ganin Ofishin Jakadancin Amurka ya amice su yi aiki tare don wayar da kan ’yan kasa kan zaben 2023.
(NAN)